~~CIGABA~~ ***ABDULJABBAR
SARKIN COPY AND PASTE (B)***
SHIN KO KUN SAN MONITAN YAN
KOGO BAYA TAHQIQIN MAGANA IN
YA KWAFO!
Hassan Farhan
Almaalikiy vs Abduljabbar Nasiru
Alkabariy >>>:
DWA'FADDAALIBU
WALMADLUUB!
Mai sauraro a baya
mun tsaya wajen da Abduljabbar
ya kwafo qaryar Almaalikiy kan
wai #Hanaabilah maqiya
sayyiduna Aliyyu (ra) ne!
ta inda
wancan bahathi ya taqaitu ne
wajen dirtse wannan mai "copy
and paste" ta fuskar sato wannan
fasaha da yayi.
yanzu kuma
Inshaa Allahu, za mu warware
wannan qaryar ne!
Mai saurare
ka ji siffar wadannan bayin Allah
wanda don tsabagen bin
Alqur'ani da Hadith, sai da ake
kiran jagoransu da Imam Ahl
Assunnah!
Kenan, duk wanda ka ji
yana sukansu, yana sukansu ne,
don riqonsu da sunnah da kuma
fakewa da sukar wani sashe na
ahlussunnah don tsabagen
taqiyya,
amma a zahiri yana sukar
jumhurin ahlussunnah ne!
HASSAN FARHAN ALMAALIKIY YACE:
" ﺃﻥ ﺍﻟﺤﻨﺎﺑﻠﺔ ﻟﺪﻳﻬﻢ ﺣﺴﺎﺳﻴﺔ ﻛﺒﻴﺮﺓ ﻣﻦ ﺍﻟﺜﻨﺎﺀ ﻋﻟﻰ ﺃﻣﻴﺮ ﺍﻟﻤﺆﻣﻨﻴﻦ ﻋﻠﻲ ﺑﻦ ﺃﺑﻲ ﻃﺎﻟﺐ
domin ba zan
batawa kaina
lokaci wajen waccan satar fasaha
ta sarkin kogo ba!
Abun
da zan tambayi Hassan Almaalikiy,
tunda dai " Albayyinatu alal
mudda'e"
A ina ka samo wannan
magana?
Na san saboda
kasancewarta qarya, shi yasa
baka sa'ba misali ba, hatta shi ma
gyauron shi'ar naka sarkin kogo,
bai kawo waje guda daya da zai
zamo hujja ba!
Lallai na gasgata fadin MAL.
MUHAMMAD BN ABY YA'ALA DA
YACE AKAN AL'IMAM AHMAD:
" ﺇﻧﻪ ﻣﺎ
ﺃﺣﺒﻪ ﺃﺣﺪ- ﺇﻣﺎ ﻣﺤﺐ ﺻﺎﺩﻕ, ﻭﺇﻣﺎ ﻋﺪﻭ ﻣﻨﺎﻓﻖ- ﺇﻟﺎ ﻭﺍﻧﺘﻔﺖ ﻋﻠﻴﻪ ﺍﻟﻆﻨﻮﻥ , ﻭﺃﺿﻴﻔﺖ ﺇﻟﻴﻪ ﺍﻟﺴﻨﻦ ﻭﻟﺎ ﺍﻧﺰﻭﻯ ﻋﻨﻪ ﺭﻓﻀﺎ
Dabaqaat alhanabila 1/15.
Lallai kam danbidi'ah ba zai so
Asshaybaniy ba kuma dole ya
dinga tufka da warwara!
Ji dai
yadda monitan kogo yace:
wai
Hanbaliyya suna tauye matsayin S.
Aliyyu don kawai shi'a sun qetare
iyaka sun soki wadanda su kafi S.
Aliyyu falala, kamar S. ABUBAKAR
da Umar da Usman...!
Ga yadda ya
ce:
" ﻭﺍﺯﺩﺭﺍﺋﻬﻢ ﺑﻤﻨﻬﻢ ﺃﻓﻀﻞ ﻣﻨﻪ ﻣﻦ ﺍﻟﺼﺤﺎﺑﺔ ﻣﺜﻞ ﺍﻟﺨﻠﻔﺎﺀ
NACE:
HODIJAM!
Copy and paste baiyi ba,
yau ga sarki na fifita Khulafa'u
akan S. Aliyyu bayan kuma a
wurare da dama yace shine a
gaba,
kai harma ya nuna su ukun
ba suyi khalifanci daidai ba!
A raddin da yake riyawa ya yiwa dr. SANI yake
cewa:
"sayyadi ALI yazo ya tarar
khilafa ta sakwarkwace yayi nufin
yagyara ta!
ya kuma cewa: "da s.
ALI ya karbi khilafar a farko to
shine zai iya yinta bisa tsari na
annabta..."
Da sauran
maganganunsa da suke nuna
fifitawarsa ga s. ALI akan s.
ABUBAKAR da dukkan sahabbai..!
MAI SAURARO DA'AWAR NASBU GA HANAABILA QARYA CE DA BA TA DA TUSHE BALLE MAKAMI, MATSALAR DA MONITAN YAN KOGO YA SAMU BAYA BIN MAGANA BISA TAHQIQI IN YA KWAFO!
Alhamdulillah wassalatu wassalamu ala rasulillah.
CIGABA~~ ***ABDULJABBAR
SARKIN COPY AND PASTE (C)***
MAQARYATA GUDA BIYU!!!!!
Hassan Farhan
Almaalikiy vs Abduljabbar Nasiru
Alkabariy >>>:
Mai sauraro a baya
mun tsaya wajen da Abduljabbar
ya kwafo qaryar Almaalikiy kan
wai hanabila suna qyashin su yabi s. Ali... wanda jawabi akanta ya gabata..
yau kuma zamu waigi shi kuma sarkin satar fasahar don amsa tasa tuhumar.,
: SARKIN kogo yace:
WAI hanabila duk inda suka sami falalar s. ALI suna rusheta ( su qaryata ta) ....
"ﻭﺇﻧﻤﺎ
ﻳﺘﺼﺪﻭﻥ ﺑﺎﻟﻬﺠﻮﻡ ﻋﻠﻰ ﻣﻨﺎﻗﺒﻪ ﻟﻘﻤﻊ ﻏﻠﻮ ﺍﻟﺸﻴﻌﺔ ﻓﻴﻪ".
muqaddima 2/663.
NACE:
# #alagatta mal. kaima MAI yahana ka bamu misali na inda su hanabila suke rushe falalolin s. ALIN indai ba qarya ka zulaqa msuba??
lallai kam wannan qarya ce cikakkiya;don abun yasake fitowa filinema zan dan bamu misali, kamar haka:
!: banda gudun tsawaitawa da na ambata litattafai goma zuwa sama da haka na hanabila din, wanda cike suke da ambaton falolin s. ALI, amma dukda haka zan bada misalai koda guda biyune,gasu kamar haka:
**M. AJURRIY acikin littafinsa ASSHARI'A ya qulla babi ya amabace shi da:
ﻓﻀﺎﺋﻞ
أﻣﻴﺮ ﺍﻟﻤﺆﻣﻨﻴﻦ., aqarqashinsa yayi fasali sama da goma wanda dukansu falaloline na s. ALI, daga cikinsu:
!: ﺑﺎﺏ ﺫﻛﺮ ﺟﺎﻣﻊ ﻣﻨﺎﻗﺐ ﻋﻠﻲ ﺑﻦ أﺑﻲ ﻃﺎﻟﺐ.
!!: ﺫﻛﺮ ﻣﺤﺒﺔ ﺍﻟﻠه ﻋﺰ ﻭﺟﻞ ﻟﻌﻠﻲ ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻪ ﻭﺃﻥ ﻋﻠﻴﺎ ﻣﺤﺐ ﻟﻠﻪ ﻋﺰ ﻭﺟﻞ ﻭﺭﺳﻮﻟﻪ.
^: ﺫﻛﺮ ﻣﻨﺰﻟﺔ ﻋﻠﻲ ﻣﻦ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﻛﻤﻨﺰﻟﺔ ﻫﺎﺭﻭﻥ ﻣن ﻣﻮﺳﻰ.
dasauransu..
bayan ya gama da ambaton falalolinnasa ne kuma yadora da kawo falalolin s. fadima, sannan kuma yakawo na hasan da husain..
wanda kuma mabiyin hanbaliyya dinne.
!!: shi kansa imam AHMAD ya bude musnad dinsa da ambaton hadisan halifofin shiriya, wanda cikinsu harda .s ALI, yakuma ambata hadisansa sama da dari takwas aciki, bayanshi kuma ya ambaci ahalal baiti...
YA dan uwa!! INA batun kuma ace wai suna goge hadisan s. ALI da falalolinsa, wannan wacce irin qaryace haka??
MAI karatu kayi alqalanci.
2: shin akwai wanda yakai mutuminda zai ware jikokin ma'aiki daga cikin sahabbansa qiyayya ga ahlil baiti kuwa????
To shi farhan dindai shine wanda yace suhba ta taqaitane ga ansaru da muhajirun, wanda baya cikinsu ba sahabi bane, kuma dai sn hasan da husain ba sa cikin biyunnan, to ya kenan???
Ashe shi wanda ake sato litattafansa azuba a muqaddima shine ahaqqu da a kira shi nasibi.
3: NI A IYA SANINA BANSAN CIKAKKUN NAWASIB BA KAMAR YA'N SHI'A; DON SUNE SUKE KIRAN S. HASAN DA " WANDA YA TOZARTA MUSULMI".
SUNE WADANDA BATANCINSU B WAI IYA GA S. ALI YATSAYA BA, HATTA MA'AIKI SAIDA YASHA NASA.. BARI NABADA MISALI DAYA:
* majlisiy ya rawaito cikin bihar cewa: sayyadi ALI yana kwantawa atsakanin ma'aiki da s. AISHA, kai suna ma rufa a mayafi guda.
BIHAR 2/30..
wanda wannan ba karamin cin zarafin ma'aiki bane, ace wani zai rufa da matarka abargo; saboda tsabar munin hakanfa, aqidar shi'a idan aka kama mutum ya rufa da wadda ba matarsa ba, to sai anyi masa bulala dari fa..
alkafiy 7/181.
amma ahaka sukace s. ALI yana rufa da matar ma'aiki.
4: ya gama zuzuta cewa hana bila suna guluwwi ga imaminsu, zaima kawo inda hakan ya auku, sai kuma yakawo rubbiyar ruwaya, wadda mudauka ma ta inganta, babu wani abu da shi zaice guluwwi ne..
qololuwar abinda ruwayar ta nuna shine: tabbarruki akayi da shi imam Ahmad din, wanda kuma mun sani tabbarruki ya halatta agun sarkin kogo.
BABBAN abun tausayin kuma:
ruwayar da yakawo ruwaya ce wadda akace imam shafi'ine yayi tabbarrukin, ni kuma sai nake tambaya:
*shin dman mal. SHAFI'I dan hanbaliyya ne ya jama'a???
WANNAN amsar zanso atambaya min ya'n aji daya a islamiyya , sune zasu amsa ta.
BAYANI dalla dalla gameda ruwayar dakuma bayyana baqin jahilcin sarkin kogo zaizo, idan nazo warware ruwayar tukunna.
5: ya kwatanta hanabila da shi'a, yace hanabila basu gaza shi'a ba wajen guluwwi ..
amsar wannan gabar tana nan zuwa acikin rubutu nagaba.
ZAMU CIGABA!!!!!
Alhamdulillah wassalatu wassalamu ala rasulillah.
**SARKIN COPY AND PASTE! D**
Misbahu Abdullahi
~~~~ CIGABA~~ ABDULJABBAR
SARKIN COPY AND PASTE (D)
DUHU NA DUKAN DUHU!!!!!
Hassan Farhan
Almaalikiy vs Abduljabbar Nasiru
Alkabariy >>>:
mai sauraro a rubutunda ya gabata mun alqawarta kawo misalan guluwwi (wuce gona da iri) na ya'n shi'a, wanda dukda haka monitan kogo ya murje idonsa yace kai daya suke da hanabila...
ga misalan maganganun shi'a din:
atayani qirgawa (
ga misalan maganganun shi'a din:
) """::::::::
1:khumaini yace: " matsayin imamansu ko annabi mursali da mala'ika basu kaishiba:
"ﻳﻨﺒﻐﻲ ﺍﻟﻌﻠﻢ أن ﻟﺄﺋﻤﺘﻨﺎ ﻣﻘﺎﻣﺎ ﻟﺎ ﻳﺒﻠﻐﻪ ﻣﻠﻚ ﻣﻘﺮﺏ ﻭﻟﺎ ﻧﺒﻲ ﻣﺮﺳﻞ".
alhukumat al islamiyya 52.
2: Qasar kabarin husaini maganin kowacce cutace:
"ﻃﻴﻨﺔ ﻗﺒﺮ ﺍﻟﺤﺴﻴﻦ ﺷﻔﺎﺀ ﻣﻦ ﻛﻞ ﺩﺍﺀ".
bihar 92/129.
awata ruwayar:
"ﻭﺃﻣﺎﻥ ﻣﻦ ﻛﻞ ﺧﻮﻑ ﻭﻫﻮ ﻟﻤﺎ أﺧﺬ ﻟﻪ".
bihae 92/131.
3: duk wanda yayi inkarin imamancin koda daya ne daga imamansu to ya zama arne, za'a tsaida masa hukuncin mai ridda.
Mufid yace:
"ﺍﺗﻔﻘﺖ ﺍﻟﺈﻣﺎﻣﻴﺔ ﻋﻠﻰ أن ﻣﻦ أﻧﻜﺮ إﻣﺎﻣﺔ أﺣﺪ ﻣﻦ ﺍﻟﺄﺋﻤﺔ ﻭﺟﺤﺪ ﻣﺎ أﻭﺟﺒﻪ ﺍﻟﻠﻪ ﻟﻪ ﻣﻦ ﻓﺮﺽ ﺍﻟﻂﺎﻋﺔ ﻓﻬﻮ ﻛﺎﻓﺮ ﻣﺮﺗﺪ ﻋﻦ ﺩﻳﻦ ﺍﻟﺈﺳﻠﺎﻡ".
bihar 89/23.
4: an baiwa s. ALI jarumtarda ko annabi bai sametaba.
7: ALIYU ubangijine daga cikin Allolinsu, zakuma akafa masa kujera yayi hisabi ranar qiyama.
biharu 39/348.
akwai maqda'i a youtube wanda malinsu yake tabbatarda wannan gabar.
5: tilasne a la'anci s. ABUBAKAR da umar idan za'ayi addu'a..
HASHIMUL bahrani a muqaddimar burhan 39 yace:
"ﻭﻓﻲ ﺍﻟﺪﻋﻮﺍت ﺍﻟﻜﺜﻴﺮﺓ ﻟﺼﻨﻤﻲ ﻗﺮﻳﺶ
SARKIN KOGO YADORA DA FADINSA:
zai taqaitane ga hanabila kadai;saboda guluwwinda ke ckn sauran mazhabobi bai kai na hanabila ba...
yace:
"ﻟﺬﺍ ﺍﺛﺮﺕ ﺃﻥ أﻗﺘﺼﺮ ﻋﻠﻴﻬﻢ ﻛﻀﺮﺏ ﺍﻟﻤﺜﻞ.,".
muqaddima 2/663
bayan ya alqawarta cewa zai dora hannunmu akan misalai na guluwwin hanabila, irin wanda shi'a sukeyi sai yace:
"ﺟﺎﺀ
ﻓﻲ ﻛﺘﺎﺏ ﺍﻟﻤﻨﻬﺞ ﺍﻟﺄﺣﻤﺪ ﻓﻲ ﻣﻨﺎﻗﺐ ﺍﻟﺈﻣﺎﻡ أﺣﻤﺪ 1 ص 120 ﻭﻛﺘﺎﺏ ﻣﻨﺎﻗﺐ ﺍﻟﺈﻣﺎﻡ أﺣﻤﺪ ﻟﺎﺑن ﺍﻟﺠﻮﺯﻱ ص أن ﺍﻟﺈﻣﺎﻡ ﺍﻟﺸﺎﻓﻌﻲ أﺧﺬ ﻗﻤﻴﺺ ﺍﻟﺈﻣﺎﻡ أﺣﻤﺪ..,
muqaddima2/663.
imam shafi' ya dauki rigir imam ahmad yana tabarruki da ita...
NACE:
lallai muna da abubuwan dubawa awannan gabar dadama, zan taqaita su cikin sadrori kamar haka:
1: fadinsa: "ﺍﻟﻨﻬﺞ ﺍﻟﺄﺣﻤﺪ ﻣﻨﺎﻗﺐ ﺍﻟﺈﻣﺎﻡ أﺣﻤﺪ".
iyakar bincikawata nidai ban sami littafi da wannan sunan dai da ya ambata ba gaskiya, hakane yasanya tilas nayi tambayoyi kamar haka:
*wane mai littafin?? WACE madba'ace ta bugashi kuma awace shekara?? Don ni kam iya bincikawata ban sameshi ba.
ataimaka aqareni da amsar nan.
2: mudauka ma wannan ruwayar ta inganta, sai nake cewa:
ai qololuwar abinda ruwayar take nunawa shine: shafi'i yayi tabarruki da imam Ahmad, wanda a iya saninmu ai tabarruki da salihan bayi abun sone agurinku kuda ya'n tawagarku.
Yaushene kuma to tabarruki yatashi daga abun so, har yazama guluwwi??
mun sani cewa akaratukanka ba adadi kayi magana akan halacin tabarruki, hakanan aqidarku taqunsa, wannan aqida halifan mahaifinkama ya tabbatar da ita cikin ﻣﺮﺃﺓ ﺍﻟﺼﺎﻓﻴة , to don me zakazo kace mana ta zama guluwwi?
OGANKU kausariy shi har kasar kabarin mutum nagari yahalatta ayi tabarruki da itama ba wai rigarsa ba, wanda ya rubuta shafuka don baiw wannan aqidar taku kariya,
DAN uwa duba maqalatul kausariy shafi na 248 kasha kallo..
ga misali:
"ﻭﻟﻬﺬ
3: idan mun yarda cewa qissar ta tabbata, shafi'i yayi tabarruki da imam AHMAD wanda hakan yasanya kai mai muqaddima ka daidaita su da shi'a,(kace kai daya suke) to sai ince maka:
indai wannan ne hujjarka ta dai-daita hanabila da shi'a to kuwa suma hanafiyya ya kamata kahada dasu; don kuwa ba su kadaine aka rawaito irin wannan tatsuniyar akansuba- bayan sam bata ma ingantaba-
suma hanafiyya din an rawaito cewar shafi'in yayi tabarruki da qasar kabarin ABU hanifa har yana cewa:
إﻧﻲ ﻟﺄﺗﺒﺮﻙ ﺑﻘﺒﺮ أﺑﻲ ﺣﻨﻴﻔﺔ..
tarkhu bagdad 1/123.
dukda cewa ruwayar ni aguna bata tabbataba, amma kai agurin ubangidanku kausariy ai ta inganta, idan kakoma shafinda na ambata maka, zakaga har tirjiya (kausariy) yayi don tabbatarda cewa ruwayar ta inganta.
tambaya anan: su hanafiyya mai yasa anan baka zargesu ba??
Amsar wannan tambayar kawai itace:
inda yaje yakwafo basu ambaci hanafiyya ba, shi kuma daman sarkin kuri da bahasin wasune, shi yasa ya kuntuka wannan shirmen.
YA dan uwa!! ananne maganata da tagabata zata sake bayyana gareka nacewa: kawai ya'n bid'a daman ba sa ga maciji da imam AHMAD... sannan kuma maganar shehi qadiy iyad zata sake bayyana garemu " yana daga alamarda za'a gane cewa mutum dan bid'ane, asameshi yana sukan malaman hadisi".
Ci gaban amsoshi gameda wannan shirmen sarkin masu wa'azin shi'a yana tafe asauran rubutuka masu zuwa insha allah.