XtGem Forum catalog
MisbahuAbudullah 1
M.misbahu pic
Barka da zuwa
ShafimaiAlbarka

Wannan Shafi Yana Zuwa Muku ne Daga Dan Uwanku

Misbahu Abdullahi Al'athariy


→Home
→Rusa Kare rayin Sarkin Kogo
→Samuwar Ibn Saba'!
→Ba Anan Take Ba!!!
→Sarkin Copy And Paste
→Ahlul Bait Basa Ragawa Y'an Shi'a
→Addinin Shi'a
→Tattaunawa
→Watan Azumin Tsofaffi Sunnah & Bidi'a
→Karayar Mukabala a Misra
→Shi'anci Da Sufanci
→Un Categories




DUK DUNIYA SUN KASA TARAR ARNE RASHIDIL MAGRIBIY???
DUK AZ'HARAWAN SUNYI TSIT DON SUN SAN BASUDA AMSA???
KU KAIWA SALAFAWAN IDAN SUN RASA AMSA SAI KUDAWO NI IN BAK????
qarya ko neman suna??????
bismillahirrahmanirrahim.
SARKIN wa'aziy a jawabinsa yayi wadannan maganganunda kuka gani a taken rubutuna (kodai wasu maganganu masu qunshe da wannan ma'anar) ... wanda kuma daga baya yazulaqawa yaransa qarya yace: bazai iya jurewa ba, yayi azamar zuwa domin tarar wannan arnen...
##### ni kam sai nakasa gane me sarkin yake nufi dacewa duk an kasa tarar arnen, shin yana nufin yin munazara da arnen aka kasa???
idan haka yake nufi sai ince gaskiya malam qarya kakeyi...
ga misalai da zan bayar na wadansu cikin munazarori da akayi dashi arnen:
1: halqa ta 315 dakuma 270da 271,,, duk munazarori ne akayi dashi.
danna qasa don ganewa idanunka:
m.youtube.com/watch?v=ZN874tZ0LOE&itct=CAUQpDAYCiITCLyOq9ifocUCFSoGcAod-18AhTIHcmVsYXRlZEiKg8WL1biwrwg%3D&hl=en&client=mv-google&gl=EG
2: almarkazul islamiy a sudan sun turo Ammar salih musa, wanda sukayi zma biyar ajere dashi rashid din..
3: akwai abinda akayi masa take da ﺑﻴﻦ ﺍﻟﺸﻴﺦ ﻃﺎﺭﻕ ﻭﺍﻟﺄﺥ ﺭﺍﺷﺪ.
idan kaduba link din dayake sama zaka samesu dukansu.
### ko kuwa sarki yana nufin raddi a rubuce dakuma baki??
idan wannan yake nufi sai ince wallahi malam qarya kakeyi!!!
1: akwai tarin shafuka wadanda aka budesu na musamman don raddin shubhohin wannan tashar...
ga misali:
soutalhaq.net/forum/forumdisplay.php?f=68
LEQA nan kagani:
http://www.youtube.com/watch?v=okphA5vCJQA&feature=youtube_gdata_player
2: akwai Abu umar albahis wanda shafi yabude na musamman don raddin shubhohin wannan tashar arubuce dakuma sauti.. sunansa ﻣﻜﺎﻓﺢ ﺍﻟﺸﺒﻬﺎﺕ
Ga misalai:
leqa can qasa idan ka shiga link dinda nakawo..
https://antishubohat.wordpress.com/
QARA da wannan:
m.youtube.com/watch?v=FviO8dyWrI4&itct=CAgQpDAYCSITCNiOxMqfocUCFQjJcAodCC8AQjIHcmVsYXRlZEjS7JPczbDqhf8B&gl=EG&client=mv-google&hl=en
** saboda yanda abu umar yataso rashid agaba shi kansa rashid har zaginsa yadinga yi awasu cikin shirye-shiryensa, misalan haka suna dadama, amma don ganewa kanka wasu daga ciki, zaka iya leqawa nan:
http://www.youtube.com/watch?v=5HO6ZZoi4fw&feature=youtube_gdata_player
AZ'HAR DAKUMA AZ'HARAWA!!!!!!.
duk az'har sun kasa sai sarkin wa'azine zai iya..
nidai wallahi a iya dan qaramin sanina, bansan wani gari da suka himmantu wajen raddin duk wasu shubhohi wadanda zasu kawo suka ga musulunci kamar qasar misra....
wanda riddikan sun hadarda munazarori, rubututtuka, dasauransu.
SAI gashi an wayi gari az'har sun kasa tarar wanga arne..
Ai itama wannan maganar kai ka san qaryace...
GUDUNMAWAR AZ'HAR WAJEN HANA MASU KAWO CIKAS GA ADDINI RAWAR HANTSI.
1: RUBUTUTTUKA:
agabana yanzu haka akwai tarin sunaye na litattafai wanda az'har tasamar, wadanda anyisune don martanin shubhohin rashid shida kakanninsa, zan taqaita ga misalai biyu kawai anan barin:
farko: akwai littafi mai suna:
ﺭﺩﻭﺩ ﻋﻠﻤﺎﺀ ﺍﻟﻤﺴﻠﻤﻴﻦ ﻋﻠﻰ ﺷﺒﻬﺎﺕ ﺍﻟﻤﻠﺤﺪﻳﻦ ﻭﺍﻟﻤﺴﺘﺸﺮﻗﻴﻦ.
wanda daya daga cikin frofesoshi na qismin hadisi da wasu malaman sukayi masa muqaddima.
littafin ya tattaro shubhohi guda 500 yayi raddinsu..
wanda kuma zaka samu da yawan shubhohin rashid anyi martaninsu acikin littafin.
AMMA DUKDA WANNAN HIMMAR SHI SARKI YACE SUN KASA.
Na biyu:
shekara dari da suka gabata anyi mutumi mai suna SAMUEL.... aqasar indiya, kiristane wanda ya shagaltu da da'awar yada kistanci...
Ashekarar 1895 ya shiga qasar misra atare dashi akwai mataimakansa acikin aikinsa na yada kiristanci, suka duqafa wajen aikin tattara dukkan wata shub'ha wadda zata kawo suka ga musulunci da musulmai....
sukayi nasarar kammala littafi wanda yafito a mujalladai guda hudu, suka sanyawa littafinnasu suna: ﺍﻟﻬﺪﺍﻳﺔ...
cikin ikon Allah sai littafin nasu yaqi samun karbuwa takowanne bangare; a saboda hakanema littafin yamutu yazamto kamar ba'a yishiba..
bayan faruwar hakan da shekara dari sai aka samu wata jam'iyya ta masu bincike na kiristoci a NISMA, qungiyar tasu tayi qoqarin daukar shi wancan littafi mai suna: ALHIDAYA -tunda ana ganin shine babban kundi da yatara shubhohin masu sukan musulinci- sai suka dinga dauko mas'alolin littafin suna tsittsinka su, suna yiwa kowacce mas'ala littafi qarami (kutayyib)...
daga cikin mas'alolinda suka buga-amatsayin dan qaramin littafi- daga cikin littafin hidaya akwai mas'ala mai taken:
ﻫﻞ ﺍﻟﻘﺮﺍﻥ ﻣﻌﺼﻮﻡ???
AKAYI nasara kuwa littafin yafado hannun kulliyyar USULUDDIN, atake alokacin kulliyar ta rarraba littafin ga wadanda suke yin karatun masters;don suyi masa raddi wanda shine zai zama risalarsu ta m.a .
bayan wadannan dalubai sun kammala aikinsune sai AZ'HAR taduba taga ai bai kamata aqyale ainihin shi wancan littafinda kowa yake sato fasahar daga cikinsaba, nan take suka sake samarda majmu'a ta malamai matasa wadanda zasuyi aikin yiwa shi ainihin littafinda rashid da iyayen gidansa suke kwafowa aciki sufito suyi burgar aiki dashi...
daga cikin wadanda sukayi wannan aikin akwai dr. Muhammad dawud da wadansunsa...
cikin ikon Allah suka fitarda littafi cikin mujalladiy 20 mai suna ALBAYAN, wanda aciki suka lallasa shubhohin wadancan arnan sukayi raddinsu, tare da nassaqa kowace shubha zuwa ga inda aka satota kafin su wadancan masu littafin hidaya dinma.
littafin kuma gaba dayama ba'afi shekara guda da bugashiba.
Wannan bayanin na taqaiceshi daga wata halqa ta Abi usamal az'hariy shida jifry..
DON ALLAH INDAI BA MAQARYACI BA WANE ZAICE AZHAR TA RASA YANDA ZATAYI DA ARNE RASHID?? BYAN INDA YAKE SATO SHUBHOHIN NASA KANSA ANYI RADDINSU????
2: TSARIN KARANTARWA.
daga cikin kulliyyoyin az'har akwai kulliyyoyinda suke da madda ta musamman akan abinda yashafi shubhohin wadancan arnan dakuma yanda za'ayi raddinsu.
3: LOKACI BAYAN LOKACI SUNA SHIRYA TARUKA NA MUSAMMAN AKAN ABINDA YASHAFI IRIN WADANNAN ARNAN DAKUMA SHUBHOHINSU.
taronsu na kusa-kusannan shine wanda sukayi acikin wannan shekarar 2015 din, leqa qasa kagani:
www.ahram.org.eg/News/101492/41/NewsPrint/373531.aspx
ATAQAICE DAI!!! QARYACE KAWAI TARE DA NEMAN SUNA SARKIN WA'AZI YA SAMBADA.
ZAMU CIGABA.


-DUK DUNIYA SUN KASA... FB POST

RIDDA A MISRA KO DAI A MISRATA???????
qarya ko jafa'i ga musulinci????? (Misbahu Abdullahi)

Nidai gaskiya shakku ya fara aurata gameda wannan labarin na sarkin masu wa'azi....
saboda labarin cewa mutane sama da miliyan biyu sunyi ridda amisra labarine wanda sam kwakwalwa bazata karbeshiba...
Akokarina nabaiwa sarkin wa'azi uzuri, sai na bazama nashiga bincike a duniya, shin wai misra guda nawace ne???
nayi bincike iya kar yina ko akwai wata qaramar hukuma acikin najeriya mai suna misra, amma ban samu ba... sai kuwa na bazama bincike to ko akwai wani bigire wanda sunansa yayi kama da misra...
sai kuwa akayi nasara na sami wata qaramar hukuma akasar libya mai suna: MISRATA...
cikin gaggawa kuwa sai nace: wtaqila to ko nan sarki yake nufi dacewa anyi ridda amisra...
katsam kuma sai natuno cewa: ai bako dayan mutanen qaramar hukumar basu wuce 280,000 ... kaga ko rabin miliyan basu kaiba, balle su haura.....
dakaina kuma nayi nazari nace kai gaskiya ba ita bace.
wai to ko misra din a iraqi take ne??? hala dai akwai misrata a iraqi ko??
koma dai akwai to ai bana zaton adadinsuma ya kai miliyan biyu din balle har suyi riddar.
ZANSO YA'N UWA KUTAYANI NAZARIN WADANNAN ABUBUWAN:
* ahankalcema shin zai yiwu ace mashahuriyar qasa kamar najeriya ma an sami mutane kimanin dubu hamsin (50,000) sunyi ridda, kuma wai ace sama da wata guda duk duniya babu wanda yasanda wannan labarin sai mutum daya????
mu'auna abun fa!!! Qasa mai dimbin tarihi kamar misra, ace an samu mutane ba dubu dari ba, ba rabin miliyanba, kai har miliyan biyu da qari, dukkansu sunyi ridda sun bar musulunci, kumafa wai ayi samada wata daya duk duniya babu wanda yasanda wannan labarin sai sarkin wa'azi??????
*** Shin abu ne mai yiyuwa MUSULMI MILIYON BIYU su yi ridda, amma labarin bai game lungu da saqon garuruwan Musulmai ba?
zanso mudan tuna da labarin mubarak da akayi kwanakin baya anan kano, wai ba musulunci yabariba ne???
amma jaridu nawane suka buga labarin??? idon duniya kaf saida ya juyo kansa...
wai mutum guda kenan, ballantana ace mutane har miliyan biyu sun bar addini, kuma duniya tayi tsit akan haka.
ni dai gani acikin qasar misra din, kuma irina muna nan dayawa, amma ko kusa ko alama bamu samu wannan labarinba.....
** wai ma kiristocin misra din gaba dayansu su nawane???
idan aka gwama adadinsu da wadanda sarkin wa'azi yace sun koma, adadin ya zama nawa kenan???
to dan uwa shiga internet kaduba, idan kabincika zaka iske percentage din kiristociin misra din dai yana nan a yanda yake bai karuba..
kana zaton zai yiwu ace anyi ridda haka dayawa, amma qasashen arna suzuba ido ba tare da sun sanya tilas an qara lambobi a adadin kiristocin misra dinba???
**** yaushene ma akayi riddar to???
shidai sarkin cewa yayi: sakamakon shirinne yasa mutane samada miliyan biyu sukayi ridda amisra...
arubutuna najiya dai na kawo hujjojinda suke tabbatarda cewa shidai wannan shirin kusan sheakara guda cur da gabatar dashi kenan....
wai to yaushene ma akayi riddarne??? Tun shekarar da ta gabata din ko kuma yaushe???
** hm!!! har na tuna da taumal hakim wanda yaje ya karanta hadisin habbatus sauda'i:
ﻓﻲ اﻟﺤﻴﺔ ﺍﻟﺴﻮﺩﺍﺀ ﺷﻔﺎﺀ ﻣﻦ ﻛﻞ ﺩﺍﺀ...
ai kuwa yaje yasamo baqar macijiya yaci, ilai kuwa saida yasami matsala.
Allah ne yasani shin dagaskene anyi hakan ko kuma labarine dai kawai oho.
amma muma dai akano anyi hakan, sarkin wa'azi yaji ance:
ﺣﺎﻟﺔ ﺭﺩﺓ..
kawai sai yadauka ana nufin riddar barin addinin musulunci;saboda tsabar jafa'i da neman bala'i.
shidai halatu riddah sam ba ya nufin ridda daga addini, idan kuma akwai wanda yake ganin hakan kuma, to zai iya matsowa kusa nabashi shafukan jaridu wanda sukayi rubutu a irin hakan, in yaso sai yataimaka ya fassara mana.
GASKIYA!!! matuqar akace malamai zasu dinga saka yara agaba suna fesa masu qarya..
INDAI ba jafa'i ba:
mutuminda qwaqwalwarsa tayarda ta karbi labarin riddar mutane sama da miliyan biyu sakamakon shiri kwalli daya.,
don allah ya kamata irin wannan qwaqwalwar tayi inkarin musuluntar mutanen makka lokacinda annabi yaje fat'hu makka??
wannene cikin labarannan yafi cancanta kwakwalwa ta karbeshi cikin gaggawa???
ALLAH yakyauta to!!!!!!!!!
zamu cigaba!!!


-RIDDA A MISRA KO A MISRATA FB POST

MUQABALA A MISRA
DON
BAYARDA KARIYA GA MA'AIKI...
QARYA KO GASKIYA?????
bismillahirrahmanirrahim:
SHIMFIDA:
haqiqa baiwa addinin musulunci kariya tare da raddin shubuhohin mabarnata abune wanda yake tilas ga musulminda ya mallaki ikon yin hakan... wannan dabi'ar kuma itace siffarda ahlussunnah suka sifantu da ita tun tale-tale.
shi yasa da zarar an taba ma'aiki kafin kaji muryar kowa zaka iske ahlussunnah sun tunzura sun maida martani, adukkan wuraren karatukansu da minbarin jumu'a nasu.
nakan iya tunowa cewa Abdul jabbar dakansa ya shaidi mal. Ja'afar -rahimahullah- cewa: dazarar an taba ma'aiki kan kowa yayunqura zaka samu ya tunzura ya maida martani.
indai ba qwaqwalwata ta ha'inceniba kenan.
adon hakane ma lokacinda muka sami labarin sarkin gida zaije muqabala misra mukayi masa fatan alkhairi.. tare da fatan nasara...
sai dai kuma kash!!! bincike sai ya gwada mana cewa sarkin gida ya zulaqa qarairayi kashi-kashi gameda abinda yashafi wannan muqbala dayace zaije, sai gashi muqabalar ta dauki salo mai ban mamaki wanda har ya kai ga shardanta wasu maqudan kudade wanda azatona ko gina as'habul kahfi baiyi awon gaba da wadannan kudadenba...
MUKALLI NAN:
1: SARKIN GIDA YACE:
"awannan tafiyarda nayi akayi shirin, kuma anyi shine alal hawa'i mubasharatan (live)......".
2: yace: "tashar alhayat ta misra".
3: yace: sakamakon shirin an samu ridda ta sama da mutane miliyan biyu a ita kasar masar din dai, kamar yanda aljazeera suka fadi".
hakan yasanya nayi wasu tambayoyi ajiya wanda zan karkatarda rubutuna na yau yazama amsace game dasu:
** : maganar cewa awannan tafiyar da yayine akayi shirin kuma ya ganshine live qaryace surfan ya danqara, babu gaskiya aciki;domin sam shirin bama acikin shekarar nan akayishiba, kamar yanda zai fito agaba.
** shiye-shiryenda sukayi awannan shekarar wato (2015) kaf dinsu guda goma sha biyar ne, wanda sun kama daga lamba ta 391 halqarsu ta qarshe a 2015 dinnan itace mai lamba 404 , ita kuma halqar dayake maganar cewa watanda yawuce yaganta, itace lamba ta 370 (ma'ana: tsakanin wadda yake magana din, dakuma wadda suka fra yi awannan shekarar akwai tazarar halqa 21) wanda hakan yake nuna cewa tun badi akayi shirin.
DANNAN nan gurin dan ganewa kanka list din shirye-shiryenda sukayi a 2015.
m.youtube.com/playlist?list=PLeALEPpd_E-mHKgKJRZLbUX78Dp58Vory&itct=CB4QojAYACITCMb9-fWXl8UCFYsTGAodhHYAig%3D%3D&gl=EG&hl=en&client=mv-google
** shidai wannan shirin -wanda yayi qaryar cewa ba'afi wata daya dayinsaba- yana cikin jerin shirye-shiryenda sukayi ashekararda tagabata, wanda kuma shirye shiryensu na sheakarar da tawuce sun kama daga 343 zuwa 390 kamar yanda wanda yaduba list din qasa zai gani, kana danna " Previous" zakaga halqar dayayi qaryar cewa atafiyar da yayine akayita, zaka iske itace afarko,wanda hakan zai gwada maka cewa kiris yarage tashafe shekara guda cur da gabatar da ta...
leqa qasa don gani da idanunka:
m.youtube.com/playlist?list=PLeALEPpd_E-lxzd2X637-SUb8QM6ycpRI&ctoken=4qmFsgIuEiRWTFBMZUFMRVBwZF9FLWx4emQyWDYzNy1TVWI4UU02eWNwUkkaBkNDayUzRA%253D%253D
** sannan sun sanya shirin a youtube sau biyu:
nafarko: sun sakashi 07/agusta/2014. danna qasa kagani:
m.youtube.com/watch?v=kh8ie-gg68o&feature=youtube_gdata_player
Nabiyu: 17/dec/2014. danna qasa kagani..
m.youtube.com/watch?v=rHAm304gyrk&feature=youtube_gdata_player
ma'ana sam ba ma acikin shekarar nan akayishiba...
amma saboda tsabar sabawa da qarya yazo yace wai tafiyarda yayine yagano shirin.. abunda tun badi akayishi.
babban abun mamakin kuma wai shirin yasa anyi ridda amisra!!!
yaushe to akayi ridda din?? tun bara din akayi kenan ko kuwa yaushe??
shidai shirin ba yanzu akayishiba, ya tafi batun shekara gudu dayi.
wata tambaya mai muhimmanci ma:
yace wai yaga sanda suka bada dama abugo masu waya, to shi da yagani maine yahashi doka wayar alokacin???
ko kuwa yaqi kira dinne har sai yazo gida ya kururuta labarin, duk gari ya dauka, kana kuma yayi yekuwar cewa zaije yayi muqabala dasu, daga bisani afito ayada cewa sunce bazasu zauna dashi ha sai ya biya dubu ma la la gashin tumakin kano???
ko kuwa sanda suka bada damar ayi kiransu bashida tahqiqin mas'alarne shi yasa bai kirasuba???
tsakani da Allah anyi kishin ma'aiki kenan??
kana kallon ana shirin harma an bayarda damar bugo waya amma sai kaqi kiransu, kuma wai daga baya sai muji ka zo ka zuqalawa yaranka ta bayan kunne wai zakaje muqabala??
ko kuwa annabin iya na ya'n salafiyya ne, shi yasa bazaka bashi kariya ba har sai ranar da yan salafiyya suka gaza bashi kariya??
** dukkan wanda yakalli shirin zai ga cewa sarkin wa'azi qarya ta zame masa addini...
banda haka tayaya shirin yazama aqasa misra akayi, alhalin lambobin wayarda suka bayar sam babu lambar masar aciki??????
bayanin hakan kuma zai bayyana a rubutuka masu zuwa.
SHIN DAMAN KARE ANNABI SAI AN HADA DA YIWA JAMA'A KARYA?? YANZU HAKAN DAI-DAI NE KENAN???
ZAMU CIGABA,
wassalatu wassalamu alaa rasulillahi


-MUKABALA A MISRA FACEBOOK POST


*Koma Saman Shafi*

*New Update*
12345»

→Online People 1
→Adadin Maziyarta 29967

*Bayyana Ra'ayin ka*

*Home / Gida*



MisbahuAbudullah 1 1